Komawar Kwankwaso ADC barazana ce ga APC

Mai fashin baƙi akan al’amuran yau da kullum a Nijeriya, Ibrahim Sadauki Kabara, ya bayyana cewa komawar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, jam’iyar ADC babbar barazana ce ga jam’iyyar APC a Kano dama ƙasa baki ɗaya.

Komawar Kwankwaso, wanda shi ne tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, zuwa sabuwar Jam’iyyar ADC, zai ba shi damar haɗewa da tsofaffin abokan takararsa a zaɓen 2023, da suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da kuma Peter Obi, domin yin nasara a zaɓen 2027.

A rana lahadi ne Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga NNPP, a daidai lokacin da ’yan adawa ke tsara lissafin siyasarsu domin ƙwace mulki daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC, wanda zai nemi wa’adi na biyu a babban zaɓen shekarar 2027.

Sai dai Ibrahim Sadauki Kabara, ya bayyana wannan wani abu ne mai motsa tarihin siyasar Nijeriya, domin kwankwason ya daidaita sahunsa da Atiku da kuma Obi , wanda hakan zai jawa jam’iyyar APC zaizayar kuri’u.

Ya ƙara da cewa yanzu kallo ya rage ga wanda yake da tsawon rai zuwa 2027, domin gwamnati mai ci sai ta yi da gaske zata iya kaiwa ga nasara.

A ranar Sanata Kwankwaso ya shiga jam’iyar ADC, a hukumance yayin wani gagarumin taro da aka shirya a gidansa dake miller road Kano.

Post masu alaƙa

Kotun ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan shari’ar jam’iyyar ADC

Babu wata kotu da ta wanke Murtala Sule Garko daga zargin badaƙalar kudi – Baba Jibo

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta raba Naira miliyan ɗaya ga matasa 36 a shirin haɗin gwiwa na magance aikata laifuka