Sojojin Rundunar Operation Haɗin Kai sun ceto fararen hula aƙalla 157 da ’yan ta’addan Boko Haram suka sace a kan hanyar Buratai zuwa Kamuya a Jihar Borno.
Majiyoyin tsaro sun ce a ranar 30 ga Maris da misalin ƙarfe 2:50 na rana aka kai wa dakarun bataliyar sojoji ta musamman ta 135 da aka tura a Echo 1, Dutsen Kura hari yayin da suke aikin rakiyar matafiya.
A lokacin fafatawar, an gano cewa ’yan ta’addan sun sace motoci kimanin 17 ɗauke da kimanin fararen hula 157 kuma suna ƙoƙarin kai su cikin daji a kan hanyarsu ne sojojin suka cimma su.
Majiyar sojar ta ce, nan da nan aka tura sojojin da ke yankin nan take kuma suka yi nasarar fatattakar ’yan ta’addan, inda suka daƙile harin tare da tilasta musu guduwa zuwa yankin Mangari.
Sojojin sun bi mayaƙan da suka gudu zuwa cikin daji, inda suka tilasta musu barin motocin da aka sace da duk waɗanda abin ya shafa.
Wani fashewa (IED) a yankin Bula Zarma-Mangari ya jikkata wani soja, kuma nan take aka kwashe shi wani asibiti a Biu don samun kulawa.
An kai mutanen da aka ceto, waɗanda suka haɗa da maza, mata da yara, zuwa garin Buratai domin jigilar su zuwa wuraren da suka nufa domin sake haɗuwa da iyalansu.
Majiyoyin soji sun ce sojoji sun ci gaba da mamaye yankin gaba ɗaya, yayin da yanayin tsaro ba shi da tabbas.