Home » Kotu A Kano Ta Yankewa Ƴan TikTok Biyu Hukuncin Zaman Gidan Yari

Kotu A Kano Ta Yankewa Ƴan TikTok Biyu Hukuncin Zaman Gidan Yari

by Mubarak Ibrahim Mandawari
0 comment

Daga Safiyanu Haruna Kutama

Wato kotun Majistiri dake zamanta a gini mai lamba 47 unguwar Norman’s land dake ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano ta aike da wasu ƴan TikTok biyu gidan yari na shekara guda amma da zaɓin tara.

RFi ta rawaito cewa kotun ta samu ƴan TikTok ɗin biyu da laifin wallafa wasu bidiyo na rashin ɗa’a waɗanda suka ci karo da Addini da kuma tarbiyyar jihar ta Kano.

Tun farko hukumar tace fina-finai ta jihar ce ta kame ƴan TikTok ɗin biyu waɗanda aka bayyana sunansu da Ahmad Isa da kuma Maryam Musa da suka fito daga unguwar Ladanai a yankin Hotoro na jihar, gabanin gurfanar da su gaban kotun

Lauyan gwamnatin jihar Barista Garzali Maigari Bichi ya tuhume mutanen biyu da haɗa baki wajen aikata manyan laifuka baya ga wallafa saƙon da ya ci karo da tarbiyyar addini da kuma dokokin jihar ta Kano, laifukan da dukkaninsu suka amsa aikatawa.

Mai shari’a Hadiza Muhammad Hassan da ta jagoranci zaman shari’ar ta aike da mutanen biyu gidan yari na shekara guda-guda amma da zaɓin tarar Naira dubu 100 kowannensu.

Haka zalika zaman shari’ar ya hori matasan biyu da su kasancewa masu ɗa’a da kuma bin dokokin jihar da addinin Islama.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?