Kotu ta ba da belin El Rufai kan naira miliyan 100

Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El Rufai.

An bayar da belinsa ne kan naira miliyan 100 da mutum guda da zai tsaya masa kan makamancin kuɗin.

Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta bayyana tsauraran ƙa’idodin belin inda ta ce wanda zai tsaya masa dole ne ya zama mazaunin Maitama ko Asokoro da ke Abuja sannan kuma dole a miƙa wa kotu takardar shaidar mallakar wata kadara.

Kotun ta kuma sake bayar da umarni cewa dole ne wanda zai tsaya masa ya zama ma’aikacin gwamnatin tarayya da ke mataki na 17 na ɗaukan albashi sannan kuma ya nuna shaidar albashi na aƙalla wata uku.

Kotun ta umarci El Rufai ya miƙa duka fasfonsa na fita ƙasar waje da yake da su.

Mai shari’a Abdulmalik ta kuma umarce shi da ya riƙa zuwa hukumar DSS kowace Juma’ar ƙarshe ta wata domin ya cike rajista har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan ƙarar.

Kotun ta kuma gargaɗe shi kan saɓa ƙa’idojin da ta ce za su iya sa wa a soke belin da aka ba shi.

Post masu alaƙa

Kwankwaso Ya Ja Girmansa Ko Na Fara Mayar Da Martani — Abba Kabir Yusuf

Najeriya na ƙara sa ido bayan ɓarkewar Ebola a Congo

DSS ta sake gurfanar da El-Rufai kan zargin satar bayanai ta wayar Ribadu