Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta ƙaddamar sabon ofishin masu kai ɗaukin gaggawa na manyan laifuka VCRU.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta ƙaddamar sabon ofishin ƴan sanda na masu kai ɗaukin gaggawa na manyan laifuka, VCRU, wanda aka kafa a ranar 29 ga watan Afrilun 2026, bisa umarnin babban sufeton ƴan sandan Nijeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, wanda yayi daidai da dokar ƴan sanda ta shekarar 2020.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa an ƙaddamar da ofishin ne, domin fuskantar manyan laifuka da yin aiki da ƙwarewa da kuma sanin yakamata.

CP Bakori, ya bayyana hakanne da safiyar yau litinin lokacin da yake yiwa manema labarai ƙarin haske yayin ƙaddamar da ofishin.

Kwamishinan ƴan sandan, ya ce wannan sashi VCRU runduna ce ta musamman wacce take aiki da bayanan sirri, kuma an kafa ta domin magance matsalar, fashi da makami, garkuwa da mutane da satar motoci da sauran manyan laifuka da suke yiwa tsaron jama’a barazana da harkokin tattalin arziki a jihar Kano.

Ya ƙara da cewa bayan ƙaddamar da VCRU rundunar yan sandan Kano, tana ƙara ƙarfi wajen kai ɗauki gaggawa na hana faruwar aikata laifuka da hana aikata laifuka ta hanayar amfani da bayanan sirri da bincike da gurfanar da masu laifuka a gaban kotuna don tabbatar da adalci.

CP bakori, ya ce  kaddamar da rundunar ya dace da gyare-gyren bisa umarnin babban sufeton yan sandan Nijeriya game da tsaro da dogaaro da samun bayanan sirri da haɗin kan da al’umma ke basu kuma za a yi aiki da nazarin sashihan bayanai da kuma yin aiki da al’umma, tare da kafa kwamitin kula da aikace-aikacen rundunar don amincewar al’umma da suka hada da kungiyoyin farar hula da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma don karɓar korafe- korafensu.

Post masu alaƙa

Akwai haɗa bakin ƴan cikin gida a harƙallar hukumar bogi

Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da kashe Naira Tiriliyan 8.8 ba tare da an tanade su cikin kasafin kuɗi ba.

Gwamnatin Zamfara ta Jinjina wa shugaban NAHCON kan nasarar aikin Hajjin 2026