Kotu ta soke takarar Atiku Abubakar na jam’iyyar ADC

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta rushe shugabancin ADC tsagin Sanata David Mark.

Yayin yanke hukuncin alƙalin kotun Mai shari’a Peter Lifu ya kuma soke duk matakan da ɓangaren na David Mark ya ɗauka a madadin jam’iyyar.

Waɗannan matakan sun haɗa da tsayar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a babban zaɓen shekarar 2027.

Atiku, wanda hukumar zaɓen ƙasar INEC ta riga ta wallafa sunansa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, daga baya ya zaɓi tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takararsa.

Sai dai a hukuncin da Mai shari’a Peter Lifu ya yanke a ranar Alhamis, kotun ta ce kwamitin riƙon ƙwarya na ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata Mark, wanda ya shirya zaɓen fidda gwani da ya haifar da Atiku a matsayin ɗan takara ADC, a matsayin haramtaccen kwamiti ne.

Hon Nafiu Bala Gombe ne dai ya shigar da ƙara a gaban kotun yana ƙalubalantar hanyar da David Marka ya zama shugaban riƙo na jam’iyyar.

Kotun ta ce ƙarar, Nafiu Bala Gombe na da tushe don haka ta yanke wannan hukunci.

Nafiu Gombe ya jaddada wa kotun cewa bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Cif Ralph Nwosu, shi (Gombe) ne mutum na gaba da dokar jam’iyyar ta tadani ya zama shugabanta.

Saboda haka, daga cikin buƙatun da ya gabatar wa kotun akwai soke duk wasu matakai da aka ɗauka a madadin jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Sanata Mark.

Post masu alaƙa

Mun yi maraba da hukuncin kotu da ya soke takarar Atiku – Nafi’u Bala

Yan sanda sun kwato motar da aka sace a harabar cocci a kano

Yan sanda da ƙungiyoyi sun wayar da kan matasa kan gudanar da zaɓe cikin lumana a Kano