Kotun shari’ar addinin musulinci mai lamba 1 dake zamanta a Fagge yan Alluna, karkashin jagorancin mai shari’a , Umar Lawan Abubakar, ta umarci mataimakin sufeton jenar na yan sandan Nijeriya mai kula da shiya ta daya dake Kano da kwamishinan yan sandan jihar, da Baturen yan sanda da kuma mataimakan kwamishinan yan sanda, su hana duk wani mai siyar da makamai akan hanya, idan kuma suka same shi, su kama shi sannan su gurfanar dashi a gaban kotu.
Tunda farko jami’an yan sandan Hotoro ne suka kama wani matashi mai suna ,Halilu Ibrahim, inda suka gurfanar dashi.
An gurfanar da matashin dauke da takaddar tuhumar samun sa da tabar wiwi da kuma muggan makamai, kuma bayan karanto masa ya amsa laifinsa, har kotun ta kafa masa shaidun jin ikirari.
Alkalin kotun ya yanke masa hukuncin daurin shekaru 2 babu zabin biyan tara da kuma bulala 50, sannan zai sake shafe watanni shida babu zabin tara.
Mai gabatar da kara barista Zaharaddin Mustapha, ya roki kotun ta dauki mataki akan masu siyar da makaman barkatai harma ya dogara da sashin dake magana akai.
- Yan Sanda Sun Kama Matar Da Ake Zargi Da Koyawa Matasa Laifuka A Jigawa.
- Sojoji Sun Kashe Yan Ta’adda Da Kwato Makamai A Borno
Kotun ta amince tare da umartar mataimakin sufeton jenar na yan sandan Nijeriya mai kula da shiya ta daya dake Kano da kwamishinan yan sandan jihar, da Baturen yan sanda da kuma mataimakan kwamishinan yan sanda, su hana duk wani mai siyar da makamai akan hanya, idan kuma suka same shi su kamashi sannan su gurfanar dashi a gaban kotu.
Lamarin fadan daba da ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar Kano, inda hakan ke haifar da tsoro da razani a tsakanin al’umma, duk da matakan da hukumomin tsaro da kuma gwamnati suka ce suna dauka.

