Rundunar yan sandan jihar Jigawa, ta samu nasarar kama wata matashiya, mai suna Shamsiyya Muhammad yar shekaru 28 mazauniyar Gidan Ruwa, bisa zarginta da koyawa matasa maza da mata hanyoyin aikata laifuka.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Jigawa, SP Shiisu Lawan Adamu, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aikewa da manema labarai.
- Kotu Ta Umarci A mayar Da Sanata Natasha Majalisa
- Sojoji Sun Kashe Yan Ta’adda Da Kwato Makamai A Borno
Sanarwar ta ce an kamata ne lokacin da jami’an yan sanda suke gudanar da sintiri har suka gano sinki-sinki na tabar Wiwi guda 18 da sauran miyagun kwayoyi da aka samu a wajen ta.
Mukadadashin kwamishinan yan sandan jihar, DCP Murtala Tijjani, ya yabawa dakarunsu da jami’an bijilanti bisa jajircewar su wajen yin aiki tare.