Kotu Ta Yankewa Mai Tangaran Hukunci Bayan Samun Sa Da Laifin Kai Hare-Hare A Ofisoshin Yan Sandan Kano A Shekarar 2012

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani shugaban ISWAP Hussaini Ismaila, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan samun sa da aikata laifukan ta’addanci.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan Ismaila, wanda ake kira Mai Tangaran, ya amsa tuhume-tuhume guda huɗu da Hukumar DSS ta gabatar a kansa.

DSS ta ce Ismaila ne, ya jagoranci kai wasu hare-haren ta’addanci a Kano a shekarar 2012.

Hare-haren sun haɗa da harin Hedikwatar ’Yan Sanda ta Bompai, Barikin ’Yan Sandan Mopol a titin Kabuga, ofishin ’yan sanda na Farm Centre, ofishin ’yan sanda na Unguwa Uku, da wasu wurare.

Mutane da dama sun jikkata a yayin kai waɗannan hare-hare.

An kama Ismaila ne a ranar 31 ga watan Agustan 2017, a ƙauyen Tsamiyya Babba da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa, a Jihar Kano.

Daga nan aka gurfanar da shi a gaban kotu bisa dokar hana aikata ta’addanci ta 2013.

Shari’ar ta ɗauki lokaci saboda ɗaukaka ƙara da kuma tabbatar da bayanan da ya bayar da farko ba tursasa shi aka yi ba.

A ƙarshe, lauyoyin gwamnati sun kira shaidu biyar, ciki har da jami’an DSS da mutanen da harin ya shafa.

Da farko Ismaila, ya ƙi amincewa da laifin da ake tuhumarsa amma bayan gabatar da shaida na biyar, ya sauya maganarsa ya amsa laifin.

Lauyansa daga Hukumar LAC, P. B. Onijah, ya roƙi kotu ta yi masa sassauci, inda bayyana cewa Ismaila ya nuna nadama kuma bai son ɓata wa kotu lokaci.

A hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Nwite ya yanke masa shekar 15 kan tuhumar farko da kuma shekaru 20 kan sauran kowace tuhuma uku.

Dukkanin hukuncin za su tafi a lokaci guda, kuma za su fara aiki tun daga ranar da aka kama shi a shekarar 2017.

Alƙalin ya umarci Hukumar Gyaran Hali ta tsare shi a gidan yari da Babban Kwamandan Hukumar ya zaɓa.

Bayan ya kammala zaman gidan yari, dole a yi masa horon gyaran hali da kawar da ra’ayin ƙiyayya kafin a sake mayar da shi cikin al’umma.

 

 

Post masu alaƙa

Ɗalibai makafi 135 sun rubuta jarrabawar JAMB a Kano

Kotun Ƙoli ta ɗage Shari’ar kujerar Sarkin Kano zuwa 2027

Babbar alkalin Kano ta rantsar da sabbin alkalan kotunan shari’a su 30