Rundunar yan sandan jihar Kano, ta kama wani matashi mai shekaru 23, Isah Yusuf, da wata mota kirar Pontiac mai launin Ja, wadda ake zargin ta sata ce.
Rundunar ta ce jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane, sun kama matashin ne a ranar 25 ga Yuli, 2026, da misalin ƙarfe 11 na safe, a Kano, bayan sun samu bayanan sirri.
A yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin, ya ce ya sayi motar ce daga Jamhuriyar Nijar, ta hannun wani mai suna Ashiru Mohammed, wanda aka fi sani da Mai Gold, mai shekaru 35, mazaunin Kofar Ruwa a ƙaramar hukumar Dala Kano.
Sai dai, binciken yyan sanda ya nuna cewa an sace motar ne a Jihar Taraba, sannan aka kai ta Jamhuriyar Nijar, inda aka sayar da ita, daga bisani aka sake sayen motar tare da dawo da ita Najeriya.
Kwamishinan yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, bisa nuna ƙwarewa tare da rundunar tana fadada bincike kan lamarin.