Kotun Ɗaukaka Ƙara ta rushe tsagin APC mai goyon bayan Wike a Ribas

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Fatakwal ta tabbatar da hukuncin da Babbar Kotun Jihar Ribas ta yanke na soke babban taron cikin gida na Jam’iyyar APC wanda aka zaɓi Cif Tony Okocha da sauran mambobin kwamitin gudanarwar jam’iyyar a jihar.

Okocha da mambobin kwamitin da aka soke suna da kusanci da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.

A ranar 20 ga Disamba, 2024, Mai Shari’a S.H. Aprioku Obomanu na Babbar Kotun Jihar Ribas ya soke zaɓukan cikin gida na APC da aka gudanar a jihar, waɗanda suka samar da kwamitin da Tony Okocha ke jagoranta.

Rashin gamsuwa da hukuncin ya sa kwamitin ya shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara domin neman a soke hukuncin Babbar Kotun.

Amma da yake yanke hukunci a ranar Juma’a, Mai Shari’a Elfreida Oluwayemisi Williams-Dawodu na Kotun Ɗaukaka Ƙara na da ke Fatakwal ya tabbatar da hukuncin kotun ƙasa tare da amincewa da soke zaɓukan cikin gidan.

Wannan hukuncin na iya yin tasiri mai girma, domin duk wasu matakai da wakilcin da kwamitin Tony Okocha ya yi a madadin APC tun daga ranar 20 ga Disamba, 2024, na iya zama marasa inganci a idon doka.

Haka kuma, hukuncin na iya haifar da rashin tabbas kan matsayin ’yan takarar da wannan ɓangaren jam’iyyar ya fitar gabanin zaɓuka masu zuwa a jihar.

Sai dai kwamitin da Tony Okocha ke jagoranta ya yi watsi da hasashen cewa hukuncin yana barazana ga matsayinsa a yanzu, yana mai cewa har yanzu shari’ar tana gaban kotun da ke sauraren asalin ƙarar.

Da yake mayar da martani kan hukuncin, Sakataren Yaɗa Labarai na APC a Jihar Ribas, Chibike Ikenga, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar ya ce,  Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke hukunci ne kawai kan ƙarar wucin gadi, sannan ta mayar da shari’ar zuwa Babbar Kotun Jiha domin ci gaba da sauraron ainihin ƙarar.

Ya ce: “Shugabancin Jam’iyyar APC a Jihar Ribas ya san da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Fatakwal ta yanke a ranar Juma’a, 29 ga Mayu, 2026, a ƙara mai lamba CA/PH/523/2024 tsakanin APC da ɓangaren Okwu Joebrown Ndike.

“A cikin ƙarar, an kalubalanci hurumin Babbar Kotun da kuma cancantar shari’ar, tare da neman umarnin kotu da zai tilasta wa ɓangarorin su ci gaba da kasancewa a yadda suke har sai an kammala sauraron shari’ar.

“Babu wata barazana ga matsayin kwamitin gudanarwar jam’iyyar har sai an kammala cikakken sauraron shari’ar. Lauyoyinmu za su yi nazarin cikakken hukuncin sannan su ba da shawara kan matakin da za a ɗauka na gaba.

“Muna kira ga magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankalinsu, kuma kada su bari wasu su ruɗe su ta hanyar karkatar da gaskiyar abin da ya faru da kuma yanayin hukuncin da kotu ta yanke,” in ji Ikenga.

Post masu alaƙa

Ƴan bindiga sun sace tsohon mai magana da yawun soji a Katsina

Sojojin Najeriya sun ceto mutum 31 da aka sace a Zamfara

Gwamnonin Najeriya na duba yiwuwar mayar da mafi karancin albashi N100,000