Bayan samun nasarar da jami’an sojin Najeriya keyi a baya-bayan nan kan yaƙi da ƴan fashin daji, Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu yace za’a cigaba da farautar ‘ƴan bindigar da suke addabar al’umma matsawar basu miƙa wuya ba.
Shugaba Tinubu ya yi wannan gargaɗi ne a jiya Alhamis, yayin ziyarar da ya kai cibiyar Sojoji ta Army Resource Centre dake Abuja, Tinubu, ya je ne domin tattaunawa a kan matsalolin tsaro da kuma hanyoyin da za’a bi wajen magance su.
Malam Nuhu Ribaɗu ne ya wakilci shugaban ƙasa, ya ce shekara 15 kenan muna fama da rashin tsaro a Najeriya. Amma yanzu lokaci ya yi da zasu dakata.
“A shekara ɗaya da ta gabata, an kashe sama da kwamandojin Boko Haram 300, sannan an samu sauƙin garkuwa da mutane domin kuɗin fansa. Don haka wannan gargaɗi ne gare su, sun dai ga yadda aka yi da kwamandojinsu, don haka idan suka ƙi miƙa wuya, za su fuskanci abun da ya faru da jagororinsu.
“Ƙofarmu a buɗe take ga duk wanda yake so ya miƙa wuya, idan ba haka ba kuma, sun san abin da zai biyo baya,”
Rundunar tsaron Najeriya dai na cigaba da samun nasara kan ƴan fashin daji da suka addabi yankunan Sakkwato Da Katsina da Zamfara, cikin nasarorin da suka samu harda hallaka ɗaya daga cikin iyayen gidan Bello Turji wato Halilu Sububu da ma wasu manyan ƴan fashin dajin.
To sai dai wasu na ganin yin maslaha da masu garkuwa da mutanen ba abu ne mai kyau ba, duba da yadda a baya aka yi sulhun kuma bai haifar da ɗa mai ido ba.