Kungiyar ACF Ta Bukaci Hadin Kan Mahukunta Don Magance Matsalolin Arewacin Nijeriya

Ƙungiyar tuntuɓa ta Dattawan Arewa wato Arewa Consultetive Forum (ACF) ta ce ya zama wajibi ta faɗawa shugabanni gaskiya don ganin sun yi abinda ya dace wajen magance matsalolin da ƴan Arewa ke fuskanta, na rashin Tsaro, da fatara, da farfaɗo da tattalin arziki da kuma samarwa Matasa aikin yi a yankin.

Shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar tuntuɓar juna ta Dattawan Arewa, (ACF) (Wazirin Dutse) Alhaji Bashir Muhammad Ɗalhatu, ne ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki, wanda ƙungiyar shiyyar Kano ta shirya na wuni ɗaya da aka gudanar ranar Asabar 09 ga Agustan 2025, a Kano.

Taron dai ya mayar da hankali ne akan bada shawarwarin da za a magance matsalolin da suka addabi yankin Arewa, da suka haɗar da matsalar Tsaro, da illar Shaye-shayen miyagun Ƙwayoyi, da faɗan Daba, da kuma fashin Waya, gami da satar Yara zuwa kudancin ƙasar.

“Ƙalubalen da yankin Arewa ke ci gaba da fuskanta sai dukkanin shugabanni a yankin sun tashi tsaye Sannan za a kawo ƙarshen su, suma kuma al’umma sai sun bada tasu gudunmawar, in ji shi”.

Da yake nasa jawabin shugaban ƙungiyar Arewa Consultetive Forum, shiryyar Kano, Dr. Gwani Farouk Umar, ya ce daga cikin matsalolin da ake dubawa har da ƙalubalen faɗan Daba, fashin Waya da kuma shaye-shayen kayan maye da ke damun jama’a a Kano, don bada shawarwari ga mahukunta da za a kawo ƙarshaen matsalolin.

A nasa ɓangaren babban kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun Ƙwayoyi ta ƙasa reshen jihar Kano (NDLEA) Abubakar Idris Ahmad, ya ce ƙungiyar ta (ACF) ta gudanar da taron ne a kan gaɓa, duba da yadda ake fama da Shaye-shayen miyagun Ƙwayoyi a sassan ƙasar

A cewarsa, “Kasancewar shaye-shayen miyagun Ƙwayoyi shi ne ummul’aba’isin da ke haifar da rikice-rikicen faɗan Daba da fashin Waya musamman ma a Kano, a don haka akwai buƙatar a ƙara tashi tsaye don daƙile matsalar, in ji Abubakar”.

Al’umma da dama ne suka samu damar halarta, ciki har da Dattawan Arewa da dama, da tsohon gwamnan Kano Mallam Ibrahim Shekarau, da shugaban Majalisar Malamai ta Kano Sheikh Ibrahim Khalil, da wakilcin hukumar Hisbah a Kano, da dai sauransu.

 

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda