Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa aikin tsaro da al’umma ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsaro da zaman lafiya jihar.
CP Bakori, ya bayyana hakan ne a ci gaba da bikin ranar ƴan sandan Nijeriya ta shekarar 2026, tare da yin aiyukan hidimtawa al’umma a sassa dabam-daban na jihar.
A cewarsa lokacin da ya zo jihar Kano, a matsayin kwamishinan ƴan sanda na 47, ya fuskanci ƙalubalen fadan daba da ƙwacen waya da masu dillacin miyagun ƙwayoyi, inda suka haɗa kai da masu ruwa da tsaki da masu riƙe da masarautun gargajiya da al’ummar gari don magance matsalar.
Kwamishinan ya bayar da misalin yadda suka kama wani riƙakken dillalin miyagun ƙwayoyi da ake kira da Ɗanwawu, har suka miƙa hannun hukumar yaƙi da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLLEA tare da gurfanar dashi a gaban kotu.
CP Ibrahim Bakori, ya kuma bayyana takaicinsa yadda ake wasu matasa suke amfani da shafukan sada zumunta suna cin zarafin mutane dake tayar da rigin-rimu, inda ya ce suna iya bakin ƙoƙarinsu don tsaftace matsalar.
Ya ce a cikin aikin tsaro da al’umma ne ya sanya su ƙirƙiro Operation Kukan Kura, wanda ya haifar da ɗa mai ido wajen sanya ido da kuma kama waɗanda ake zargi da aikata laifuka masu yawa.
Ya ƙara da cewa faɗan daba da ƙwacen waya da sauran laifuka a faɗin jihar sun ragu sosai, sakamakon yadda jami’ansu suka jajirce tare da taimakon al’umma wajen yin aiki kafaɗa da kafaɗa don tabbatar da tsaro.
ya yabawa al’ummar jihar bisa haɗin kai da goyon bayan da suke basu har aka samu nasarori wajen daƙile aikata laifuka.