Rikicin Iyaka yayi sanadiyar mutuwar jami’in ɗan sanda A Wudil Kano.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta tabbatar kama waɗanda ake zargi da hannu a rikicin Iyaka da yayi sanadiyar mutuwar jami’inta ɗaya, a kauyukan Katai, Gabagadi da Faudan dake ƙaramar hukumar Wudil.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, ne ya bayyana hakan, inda ya ce rikici ne tsakanin wasu kauyuka, kuma tuni ya tattauna da shugabannin ƙananan hukumomin Wudil da Dawakin Kudu.

Anasa bangaren shugaban karamar hukumar Dawakin Kudu, Sani Ahmad Mai Rago, ya zargin dagacin garin Gajere, Abubakar Isiyaku, da haddasa rikicin da yayi sanadiyar mutuwar jami’in ɗan sandan da kuma ƙone garuruwa uku.

A cewar Sani Ahmad , dagacin ya mayar da kwatar gonakin mutanen ƙananan hukumomin Wudil da Bunkure da Dawakin kudu, hanyar azurta kan sa, har aka gurfana da shi a agaban kotu kafin ya fita daga harkar gonakin mutanen Dawakin Kudu.

An zargi dagacin da yin amfani da jami’an tsaro bisa san zuciyar sa,  ta hanyar basu bayanan karya, tare da yin kira ga gwamnatin jihar Kano da ta dauki matakin gaggawa domin kawo karshen gallazawar da yake yiwa mazauna kananan hukumomin.

 

Post masu alaƙa

DSS ta kama waɗanda ake zargi da sace Farfesa A Nasarawa

An gurfanar da waɗanda ake zargi da sace ɗaliban Oyo

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma