Jagoran jam’iyyar adawa ta NNPP kuma tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso,da tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗantakarar shugabcin ƙasar a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar sun yi tir da kisan ‘yan Arewa a jihar Edo, inda suka nemi a gudanar da bincike.
Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya bayyana harin a matsayin “rashin adalci”
Ya jaddada cewa duk wani ɗan Nijeriya na da ‘yancin yin tafiya a ƙasar nan ba tare da fargabar cin zarafi ko tsangwama ba.
“Abin da kowa ya sani shi ne, ya zama wajibi a bar ‘yan kasa su yi tafiya a duk faɗin kasar nan ba tare da fuskantar wata barazana ko cin zarafi ba.
“Ina kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike a kan wannan lamari mai tayar da hankali tare da tabbatar da an hukunta masu hannu a ciki,” in ji Kwankwaso.
A nasa bangaren tsohon mataimakin mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana kaɗuwarsa.
- Mutane 16 Da Aka Kashe A Edo ’Yan Jihar Kano Ne — Amnesty
- Kisan ‘Yan Arewa A Edo: ‘Yan Sa Kai Sun Zata Ɓata Gari Ne; Fred Itua
tare da kiran mahukunta da su gaggauta ɗaukar matakan da suka dace kan lamarin
A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya ce “ina matuƙar baƙin ciki da rahotannin kisan gillar da aka yi wa wasu mafarauta a Jihar Edo.
“Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalai da ’yan uwan waɗanda abin ya shafa.
“Wannan mummunan lamari yana buƙatar cikakken bincike domin ganowa da kuma tabbatar da cewa an gurfanar da waɗanda ke da hannu a ciki.”
Atiku ya kara da cewa “kare rayukan waɗanda da ba su ji ba ba su gani ba dole ne ya kasance abu mai muhimmanci.
“Kuma ina kira ga hukumomi da su gaggauta ɗaukar mataki don hana sake afkuwar wannan lamari na ɗaukar doka a hannu.”
