Karamin sashe na ɗaya na babban sashe na huɗu na dokar albashin Najeriya na 2019 da aka yi wa kwaskarima a 2024 ya ce biyan albashi mafi ƙaranci na naira dubu 70 bai shafi wasu ma’aikatu ba.
Sashen ya lissafo su kamar haka:
Ma’aikatun da ke da ma’aikatan wucin-gadi.
Dillalai, waɗanda ma’aikatu ke biyan su daidai da aikin da suke yi a wani ƙayyadadden lokaci.
Ma’aikatun da masu yi musu aiki ba su kai mutane 25 ba.
Ma’aikatan da ke aiki na lokaci zuwa lokaci kamar masu aikin ƙwadago a ma’aikatu ko gona.
Ma’aikatan jirgin sama ko na ruwa waɗanda dokokin aikinsu suka bambamta da sauran ka’idojin ayyuka.