Mahaifiyar shahararren mawaƙin siyasa a Najeriya Dauda Adamu Kahutu Rarara, ta shaki iskar ‘yanci tun bayan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da ita a karshen watan jiya.
Mawaƙinne ya sanar da hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram da safiyar ranar Laraba.
Rarara ya ce “Cikin yarda da amincin Ubangiji, mun samu dawowar Mama cikin aminci,”.
- Majalisa Ta Buƙaci Tinubu Ya Dakatar Da Yarjejeniyar Samoa
- Kano: Wata yarinya ta rasa ranta sakamakon haɗarin mota
A baya dai ‘yan bindigar da suka sace Hajiya Halima Adamu ƙauyen Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja sun bukaci a biya naira miliyan 900 a matsayin kuɗin fansa.
Kawo yanzu Rarara bai yi ƙarin bayani ba kan ko sai da aka biya kuɗin fansa kafin sakin mahaifiyar tasa.