Mai Martaba Sarkin Hadejia Ya Bukaci Gwamnatin Jigawa Ta Dauki Matakan Magance Barazanar Ambaliyar Ruwa

 

Shugaban majalisar sarakunan masarautun jihar Jigawa, mai martaba sarkin Hadejia, Alhaji Dakta Adamu Abubakar Maje, ya bukaci gwamnatin jihar ta daukin matakan gaggawa don magance barazanar ambaliyar ruwa , a wasu garuruwan hakiman musamman wadanda suke kusa da gabar kogi.

Mai martaba sarkin Hadejia, ya bayyana hakan ne, a ranar juma’a  a wajen maulidin tunawa da ranar da aka haifi Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam.

Ya kara da cewa a cikin garin Hadejia ambaliyar ruwan ta shafi kwata da magudanan ruwa, inda ya yi kira ga gwamnatin ta kara himma don magance matsalar, tare da yaba wa gwamnatin jihar wajen  tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma da dukiyoyin su.

Ana dai gudanar da bikin hawan sallar gani duk ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal, a masarautar Hadejia wanda ya shafe sama da shekaru 100 ana yi, haka zalika ana yin sallar ganin a masarautar Gumel dake jihar Jigawa da kuma masarautar Daura a jihar Katsina.

Bisa al’ada  mai martaba sarkin Hadejia ya kan fito bayan sallar la’asar ya zagaya zuwa wasu unguwanni don karbar gaisuwa daga al’ummarsa kafin ya dawo fada ya karbi gaisuwa daga hakimansa.

Sarkin ya sake yabawa gwamnatin jihar bisa yadda aka samu zaman lafiya tsakanin Manoma da Makiyaya, sakamakon kwamitin tattaunawa da gwamnatin ta kafa na magance matsalar yadda wasu makiyaya suke shiga cikin gonakin manoma su lalata musu amfani, inda ya tabbatar da cewa babu wani rahoto da suka samu na rikici tsakaninsu.

“Ina kara godiya ta musamman ga gwamnatin jiha domin Bama samun rahoton aikata laifuka bisa matakin da muka dauka na yin addu’a” Sarki Hadejia “.

Sarkin  ya yi kira ga jama’a da su kasance masu bayar da goyon baya don dorewar zaman lafiya a koda yaushe.

Sakataren gwamnatin Jigawa Bala Ibrahim, ne ya wakilci gwamnan jihar Umar Namadi Danmodi, ya yin gudanar bikin hawan sallar ganin.

Manyan bakin da suka halatta sun hada da , mai martaba sarkin Katagun, tsohon shugaban hukumar shigi da fice ta kasa Muhammad Babandede, Darakta janar na ma’aikatar fasaha da kara ilimi Kashifu Inuwa, babban sakataren Shari’a na kasa Malam Ahmad Gambo Saleh , kwamishinoni da shugabannin kananan hukumomin jihar da sauran al’umma daga sassa dabam-daban.

Post masu alaƙa

Kotun ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan shari’ar jam’iyyar ADC

Babu wata kotu da ta wanke Murtala Sule Garko daga zargin badaƙalar kudi – Baba Jibo

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta raba Naira miliyan ɗaya ga matasa 36 a shirin haɗin gwiwa na magance aikata laifuka