Wasu gaggan ‘yan bindiga sun kashe mutane shida tare da yin garkuwa da sama da mutane sama da 250 a wasu kauyuka na karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina a cikin kwanaki uku.
Waɗan da abin ya rutsa da su suka sha da ƙyar sun ce a ranar Lahadi da misalin karfe 11 na dare, maharan suka afka kauyen Dankurmi inda suka shafe sa’o’i hudu suna ta’addanci gida-gida. Sun kashe mutane hudu, ciki har da wani karamin yaro, sannan suka sace mutum 79.
Wasu kuma sun bayyana wa manema labarai cewa daga cikin waɗan da aka sata har da mata, yara da manya maza daga gidaje daban-daban tare da satar kayayyaki masu daraja da suka hada da babura da kayan abinci.
- Mai Martaba Sarkin Hadejia Ya Bukaci Gwamnatin Jigawa Ta Dauki Matakan Magance Barazanar Ambaliyar Ruwa
- Hisbah Ta Kama Mai Safarar Mutane Da Mata 12
Sun kuma ce adadin mutanen da aka sace a kauyukan da dama ya kai kusan mutum 200.
Waɗanda suka mutu a harin sun hada da Maharazu Sani, Awusu Shafi’u da Saminu Ibrahim, baya ga wani matashi da ba a bayyana sunansa ba.
Harin bai tsaya a Dankurmi kadai ba, domin an ce a Gamji an kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu mutane 31, sannan a Tsaunin Jino an sace mutane 27.
Wani babban jami’in gwamnati da ya nemi a ɓoye sunansa saboda tsaro ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce, mahukunta daga yankunan da abin ya shafa suna Katsina, babban birnin jihar domin lalubo hanyoyin da za a kawo ƙarshen rashin tsaron da ya addabi jama’a.