Majalisar Wakilai ta soma binciken yadda aka yi amfani da tallafin dala biliyan 4.6 da Nijeriya ta karɓa daga ƙetare a tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, domin yaƙi da cututtukan HIV/AIDS, tarin fuka (TB), da zazzabin cizon sauro (maleriya).
Wannan na zuwa ne bayan ƙudirin da Honarabul Philip Agbese daga Jihar Benuwe ya gabatar a yayin zaman majalisar na ranar Talata.
Agbese ya bayyana cewa Nijeriya ta karɓi kusan dala biliyan 1.8 daga Global Fund da kuma dala biliyan 2.8 daga Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) a tsakanin 2021–2025, sai kuma sama da dala biliyan 6 daga shirin tallafin Amurka na PEPFAR domin tallafa wa tsarin kiwon lafiya da yaƙi da cututtuka.
Sai dai ya bayyana damuwa cewa duk da wannan gagarumar gudunmawa, har yanzu Najeriya na daga cikin ƙasashen da suka fi fama da cutar HIV da tarin fuka da maleriya a duniya.
- Gwamnatin Kaduna Da Hadin Gwiwar Hukumar Bayar Da Tallafin Noma Sun Raba Manoma 400 Kayan Noma.
- Joy Ogah Ta Zama Mataimakiyar Shugaban Nijeriya Ta Rana Daya.
Ɗan majalisar ya yi gargadin cewa, muddin ba a dauki mataki ba, Najeriya na iya gaza cimma muradin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya a ƙarƙashin manufofinta na kawo ƙarshen cututtukan HIV, tarin fuka, da zazzabin cizon sauro nan da shekarar 2030.
Dangane da hakan ne majalisar ta umurci Kwamitin Kiwon Lafiya, HIV/AIDS, TB da Malaria ya binciki yadda aka kashe kuɗaɗen, tare da kawo mata cikakken rahoto nan da makonni hudu.
Haka kuma, ta buƙaci Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, da ya gabatar da cikakken tsarin aiwatar da tallafin da majalisa ta amince da shi.