Yadda Kwankwaso Ya Yi Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsa

Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanar da shirinsa na ɗaga darajar Kwalejin Jinya ta Nafisatu da ke Kwankwaso zuwa cikakkiyar Jami’ar Kiwon Lafiya albarkacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a a yayin wani taron aza harsashin ginin jami’ar a wannan Talatar, 21 ga watan Oktoban 2025, wanda ya gudana a garinsa na Kwankwaso da ke Karamar Hukumar Madobi.

Tsohon gwamnan ya yaba da ci gaban da makarantar ta samu tun daga kafuwarta a 2019 zuwa yanzu.

Kwankwaso ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin ƙara buɗe damammaki ga mata matasa su sami ilimin kiwon lafiya mai zurfi.

Ya jaddada cewa makarantar ita ce ta farko a Najeriya da ke karɓar dalibai mata kaɗai.

Ya kuma gode wa gwamnatin Jihar Kano bisa tallafa wa shirin ungozoma na Community Midwives, wanda ke taimakawa wajen inganta lafiyar mata a ƙauyuka.

A nasa jawabin, Farfaesa Saleh Ngaski Garba, shugaban majalisar gudanarwar makarantar, ya bayyana cewa kwalejin ta taimaka sosai wajen bai wa mazauna ƙauyen ilimin jinya da ungozoma, kuma yanzu tana da ɗalibai sama da 400 da suka kammala karatu.

Kwankwaso ya ce gina jami’ar zai amfanar da Kano da Najeriya baki ɗaya.

Post masu alaƙa

Gwamna Namadi ya dakatar da hadimansa huɗu

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano

Babachir Lawal ya fita daga ADC