Majalisar Dattawa Ta Amince Da Buƙatar Tinubu Na Aikewa Da Sojoji Zuwa Jamhuriyar Benin

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da buƙatar da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike ma ta na neman a tura sojojin Najeriya zuwa jamhuriyar Benin domin kwantar da tarzoma bayan wani yunƙurin juyin mulki da aka yi a baya bayan nan.

Sanatocin dai sun kaɗa kuri’ar amincewa da tura sojojin da gagarumar, inda suka bai da goyon bayan majalisa kan batun tabbatar da tsaro a yankin.

Shugaban Majalisar Godswill Akpabio ya bayyana matakin a matsayin matakin da ya dace, yana mai cewa rashin zaman lafiya a kowace ƙasa da ake maƙwabtaka da ita yana barazana ga ɗaukacin yankin.

Shugaba Tinubu dai ya miƙa buƙatar ne a cikin wata wasiƙa da aka karanta yayin zaman majalisar a ranar Talata.

A cikin wasikar, shugaba Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatin Benin ta yi gaggawar neman tallafin jiragen sama na musamman daga rundunar sojojin Najeriya bayan da sojoji suka yi yunƙurin hamɓarar da shugaba Patrice Talon.

Shugaba Tinubu ya yi gargaɗin cewa Jamhuriyar Benin na fuskantar “yunƙurin ƙwace mulki ba bisa ƙa’ida ba ta hanyar ruguza cibiyoyin dimokraɗiyya”.

Yunƙurin juyin mulkin Jamhuriyar Benin dai ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata, lokacin da wasu sojoji suka kutsa gidan talabijin na ƙasar su ka kuma sanar da tsige shugaban ƙasar Patrice Talon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *