Dan Sarkin Daura ya fito takarar dan Majalisar Wakilai

Muhammad Daha, ɗa ga Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Tarayya mai wakiltar Baure/Zango a zaɓen 2027.

Daha, wanda ke rike da sarautar Danburam na Daura, ya ce matakin ya biyo bayan kiraye-kiraye  daga al’ummarsa da ke son ya wakilce su a Majalisar Tarayya.

“Ina sanar da magoya bayana cewa na amince da kiran da aka yi min. Na yanke shawarar tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai domin wakiltar Baure/Zango a zaɓen 2027. Ina kuma roƙon magoya bayana da su guji duk wani abu da zai iya zama raini ko cin mutunci ga kowa a cikin goyon baya gare ni,” in ji shi.

Sai dai bai bayyana jam’iyyar da zai tsaya a ƙarƙashinta ba, lamarin da ake ganin na iya zama dabara. Wasu majiyoyi sun ce akwai yiwuwar ya tsaya a ƙarƙashin APC ko kuma ADC.

Muhammad Daha Umar Faruk ya shahara wajen tallafa wa matasa da kuma gudanar da ayyukan ci-gaban al’umma, musamman a fannin wasanni a yankin.

Post masu alaƙa

Ƴan bindiga sun sace tsohon mai magana da yawun soji a Katsina

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta rushe tsagin APC mai goyon bayan Wike a Ribas

Sojojin Najeriya sun ceto mutum 31 da aka sace a Zamfara