Majalissar Dattawan Nijeriya Zata Tantance Sabbin Hafsoshin Tsaro A Ranar Laraba

A gobe Laraba ne majalisar dattawa ta Najeriya za ta tantance sababbin manyan hafsoshin tsaron ƙasar da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa.

Tinubu ya aike da sunayen sababbin hafsoshin ne zuwa ga majalisa domin tantancewa kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Shugaban majalisar Sanata Godwill Akpabio ya tabbatar da karɓar wasiƙar ta shugaban ƙasa, inda ya ce kwamitin da ke da alhakin aikin zai zauna gobe ya tantance su.

Tinubu dai ya yi sauye-sauye ne a ɓangaren tsaron ƙasar, inda ya ɗaga darajar Laftanar Janar Oluyede Olupemi daga babban hafsan sojin ƙasa zuwa babban hafsan tsaron ƙasar domin ya maye gurbin Janar Christopher Musa wanda aka cire.

Sannan ya naɗa sababbin hafsoshin sojin sama da na ruwa da ƙasa, sannan ya bar babban hafsan sashen tattara bayanan sirri na sojin ƙasar, Manjo Janar E.A.P. Undiendeye

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya