A Najeriya ‘yan majalisar dokokin ƙasar sun sake zama inda suka yi karatu na biyu ga ƙudurin dokar nan da ke neman yin gyaran fuska ga dokar zaɓe ta 2022 da za ta tilasta ‘yan ƙasar jefa ƙuri’a a lokacin manya da ƙananan zaɓuka masu zuwa.
Wannan sabon ƙudurin doka dai ya janyo rarrabuwar kai a majalisar dokokin Najeriyar.
Yayin da wasu ƴan majalisar ke ganin zai zama tamkar take ‘yancin ‘yan ƙasar ne, wasu kuwa na bayyana shi a matsayin mataki mai kyau, wanda idan ya zama doka za a iya cin tara ko kuma yanke masa hukuncin zaman gidan kaso duk wanda ya ƙi yin zaɓe.
‘Yan majalisar dokokin sun gudanar da muhawara tare da tattaunawa game da shirin yin gyaran fuska ga dokar shekarar 2022 da ta shafi zabe domin tabbatar da kowane dan Najeriya ya sauke nauyin da ke kansa na yin zabe.
- Cikin Makonni Kaɗan Obasanjo Ya Murƙushe Boko Haram — Atiku
- Tinubu Ya Kaddamar Da Jirage 2 Don Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Sun bayyana cewa akwai bukatar cin tarar naira dubu 100 ga duk wanda ya ki jefa kuri’a ko kuma dauri a gidan yari nana tsawon watanni shidda ko ma duka biyu.
‘Ƴan majalisar dai sun kai ga yi wa kudurin karatu na farko da na biyu, da kakakin majalisar wakilan kasar Tajudeen Abbas ya jagoranci zaman.