Malaman turanci 337 sun fara samun horon hadin gwiwa a jihar Jigawa

Gwmnan Jihar Jigawa, Umar Namadi Dan Modi

Gwamnatin Jihar Jigawa tare da haɗin gwiwar Partnership for Learning for All in Nigeria (PLANE) sun ƙaddamar da shirin horas da malamai 337 kan koyar da harshen Ingilishi a makarantun firamare, Shirin ya shafi makarantu 132 da aka zaɓa, inda ake sa ran ɗalibai sama da 30,000 daga ajin firamare ɗaya zuwa uku za su amfana.
‎Za a horas da malamai a ƙananan hukumomin Dutse, Gagarawa, Jahun, Kafin Hausa, Malam Madori, Taura da Yankwashi.
‎Shugaban Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Jigawa, Farfesa Haruna Musa, ya bayyana shirin a matsayin mataki mai muhimmanci wajen inganta ƙwarewar malamai, ya ce fara koyar da Ingilishi tun daga ƙananan ajujuwa zai taimaka wajen shirya ɗalibai su iya shiga gasa a matakin ƙasa da na duniya.
‎A nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban Shirin PLANE na Ƙasa, Samuel Achimugu, ya ce shirin na samun tallafin Gwamnatin Birtaniya kuma ana gwada shi ne a halin yanzu, idan sakamakon ya yi kyau, za a faɗaɗa shirin a duk faɗin Jihar Jigawa tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Ilimi da SUBEB.

Post masu alaƙa

INEC ta kai wa CBN ajiyar muhimman kayan zaɓen Gwamnan Osun

Hisbah za ta fara farautar masu aikata baɗala a Kano

Rundunar yan sandan shiyya ta daya ta kama Mutane biyar kan zargin jabun magunguna da sojan Gona.