Aƙalla ’yan Najeriya miliyan 141 ne ake hasashen za su kasance cikin talauci a bana, a cewar wani rahoto da ya yi nazarin tattalin arzikin kasar a 2026.
Rahoton, wanda cibiyar tattalin arziki ta PwC ta fitar mai taken: “Juya daidaiton tattalin arziki zuwa ci gaba mai dorewa” ya yi hasashen cewa matakin talauci zai kai kusan kaso 62 cikin 100 na al’umma a shekarar da ke dab da ta zaben 2027.
Rahoton ya nuna cewa duk da sabbin manufofi da aka ɗauka don daidaita tattalin arziki, ƙarancin haɓakar kuɗin shiga na hakika da matsananciyar tsadar rayuwa na iya tura ƙarin iyalai cikin talauci a cikin shekaru biyu masu zuwa.
PwC ta kiyasta cewa yawan talauci a Najeriya zai ƙaru zuwa kaso 62% nan da shekarar 2026, wanda ke nuna tasirin raguwar kuɗin shiga da ƙaruwar hauhawar farashin kaya.
A cewar rahoton, yawancin ‘yan Najeriya ba za su samu ƙarin kuɗin shiga da zai iya rage tsadar rayuwa ba, musamman a gajeren lokaci.
“An yi hasashen talauci zai ƙaru zuwa kashi 62 cikin 100 (mutane miliyan 141) nan da 2026, saboda ƙarancin haɓakar kuɗin shiga na hakika da tasirin hauhawar farashin kaya,” in ji PwC.
Kodayake hauhawar farashin kaya na iya raguwa a hankali, PwC ta lura cewa tsarin tattalin arzikin ya nuna cewa samun sauƙin rayuwa ga iyalai zai ci gaba da fuskantar koma baya.
Babban abin da ke ƙara tsananta talauci, in ji PwC, shi ne tsarin cinikin gidaje masu sauƙin kuɗi.