“Maslahar Al’umma Gwamnati Ta Duba Kafin Rufe Makarantu Gabanin Azumi.” -Kwamishinan Harkokin Addinai

Kwamishinan harkokin addinai na jihar Kano Honorable Ahmad Tijjani Sani Lawal ya yi martani kan cece-kucen da ake yi game da rufe makarantu da wasu gwamanatocin Jihohi sukayi gabanin fara azumin watan ramadan.

Kwamishinan ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne saboda maslahar al’umma, inda ya ƙara da cewa hakan zai bawa Mutane damar yin ibada, cikin kwanciyar hankali.

Honorable Ahmad ya bayyana hakan ne cikin wata ziyara daya kawo Gidan Rediyo da Talabijin na Muhasa a yau Laraba,”Gwamnati tana da ikon yin abubuwan da za su sauƙaƙawa al’ummarta indai basu saɓawa doka ba,”a cewar sa.

An sami cece-kuce da kuma mabanbantan ra’ayoyi tsakanin al’umma dama wasu jami’an gwamnati, inda suke sukar matakin rufe makarantun Firamare da Sikandire, inda wasu suke ganin hakan ya saɓawa tsari.

Cikin tattaunawar da yayi, ya roƙi  al’umma dasu dage tuƙuru wajen yin ibada, tare da saka shugabanni a cikin adduo’insu.

 

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda