Rundunar yan sandan jihar Kano ta gaiyaci Hon. Aminu Abdullahi Warkal kan zargin nuna bindiga a wani taron siyasa.
Rundunar ta ce jami’anta sun ga wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda aka ga Warkal yana nuna wata bindiga da ake zargin Pump Action Rifle ce yayin wani taron siyasa.
A cewar rundunar, idan bincike ya tabbatar da cewa an nuna bindigar ba bisa ka’ida ba, hakan na iya zama saɓa wa dokar makamai (Firearms Act), tare da haifar da fargaba da barazana ga zaman lafiyar jama’a.
Kakakin Rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayar da umarnin gaiyatarsa.
Rundunar ta ce yanzu yana hannunta inda ake ci gaba da bincike kan lamarin.
Rundunar ta kara da cewa ba za ta lamunci rashin bin doka, daba ko nuna makamai da ka iya kawo barazana ga tsaron jama’a ba, komai matsayin wanda abin ya shafa.
sun kuma gargadi ’yan siyasa da magoya bayansu da su gudanar da harkokinsu cikin lumana, tare da bin dokar zabe da dokar makamai da sauran dokokin ƙasa.
Rundunar ta sake jaddada cewa za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da tabbatar da zaman lafiya a Kano kafin, lokacin da kuma bayan kakar siyasa.