Wani matashi ya kashe mutum uku a masallaci a yayin da suke jiran Sallar Asuba a yankin Gwarimpa das ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Matashin ya daɓa wa mai kula da masallacin da wasu mutum biyu wuƙa har lahira a yayin da suke jiran sallar ne a masallacin da ke Kado Bimko a shiyyar First Avenue da ke shararriyar unguwar.
Wani ganau, Muhammad Auwal, mai shago a kusa da masallacin, ya ce wanda aka fara kashewa, Alhaji Wanzam, dattijo ne da ke sana’ar wanzanci a kusa da masallacin.
“Alhaji Wanzam yakan zo masallaci tun ƙarfe 4 na asuba daga gidansa da ke kusa, ya buɗe masallacin, ya tsabtace harabar gaba ɗaya. Yana cikin aikin tsabtacewar ne, sai wanda ake zargi ya kai masa hari, ya yi ta daɓa masa wata sharɓeɓiyar wuƙa,” in ji shi.
Muhammad Auwal ya shaida wa wakilinmu cewa wanda ake zargin, wanda aka fi sani da Laminde Boka, bayan ya kashe Alhaji Wanzam, ya ci gaba da far wa wasu mutane da wuƙar da ke hannunsa.
Laminde Boka, wanda ake kyautata zaton yana cikin mayen miyagun kwayoyi, ya daɓa wa wani mutum da ya yi ƙoƙarin tsayawa ya fuskance shi, wuƙa. Mutumin, wanda ke da injin nika a kasuwar da ke kusa, ya rasu a kan hanya yayin da ake ƙoƙarin kai shi asibiti.
Daga bisani, wanda ake zargi ya bi wasu masu ibada, inda ya cimma wani da ya faɗi ƙasa, ya daɓa masa wuƙa har lahira.
A karshe mutane suka ritsa shi a harabar masallacin, suka yi ta jifan sa da duwatsu, kafin daga ƙarshe su buge shi da sanda, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take.
Auwal ya ce a ranar aka wuce da gawar Alhaji Wanzam zuwa garinsu, Gezawa a Jihar Kano, yayin da gawar na biyun kuma aka kai ta Jihar Katsina.
Gawar na uku kuma, wanda birkila ne daga Jihar Gombe, an kai ta ɗakin ajiyar gawa a Asibitin Kubwa a Abuja, saboda ba a samu danginsa ba har zuwa ranar Lahadi, duk da cewa al’umna su san shi a matsayin ma’aikaci.
Wani shaida ya ce an fara jefar da gawar wanda ake zargi a kan bola, kafin daga baya ’yan sanda su kai ta ɗakin ajiyar gawa na Asibitin Kubwa.
- Rundunar sojin Najeriya ta ce ta yaye ƙarin kurata 3,439
- Rundunar sojin Najeriya ta ce ta yaye ƙarin kurata 3,439
Mai unguwar Kado Bimko, Malam Ibrahim Isiaku, ya bayyana cewa bayan faruwar lamarin, masu ibada da suka saba yin barci a masallaci da kuma masu zuwa Sallar Asuba sun tsere zuwa sashen ƙauyen da yake zaune, inda suka yi sallah tare da su. Masallacin da abin ya shafa kuma an rufe shi.
Ya ƙara da cewa an gudanar da taro bayan lamarin, inda aka haɗa kwamitin masallacin, shugabannin kasuwar da ke kusa, da manajan tashar mai da ke gefen masallacin.
An cimma matsaya cewa daga yanzu ba za a ƙara bari kowa ya kwana a harabar masallaci ba, kuma duk wanda ya karya wannan umarni za a kai rahotonsa ga ’yan sanda domin a kama shi.
Ƙoƙarin wakilinmu na jin ta bakin DPO na Gwarimpa bai yi nasara ba, domin an ce ba ya ofis lokacin da wakilinmu ya kai ziyara jiya.
Sai dai wani babban jami’in ‘yan sanda ya tabbatar da faruwar lamarin