Matatar Dangote Ta Musanta Dakatar Da Aiki

Matatar mai ta Dangote ta ƙaryata rahoton da ke cewa za ta iya dakatar da ayyukanta na sarrafa ɗanyen mai har nan da tsawon watanni biyu zuwa uku.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rukunin kamfanin na Dangote, Anthony Chiejina ya fitar, inda ya bayyana rahoton a matsayin “tsantsar ƙarya” wadda ba ta da tushe balle makama.

A wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar, ya bayyana cewa, ‘‘akwai yiwuwar rufe sashen matatar man kamfanin wadda ke samar da ganga 650,000 duk rana tsawon watanni biyu zuwa uku saboda aiwatar da wasu gyare-gyare, yana mai ambato shawarar da masana’antar IIR Energy da ke sa ido kan makamashi ta bayar.

A cewar rahoton, tun daga ranar 29 ga watan Agusta aka yi ikirarin rufe sashen matatar man bayan da aka samu matsala ta kwararar mai daga ɓangaren tace man masana’antar.

Kazalika rahoton ya ƙara da cewa, matatar za ta yi ƙoƙarin sake soma aikin tace mai na ganga 204,000 duk rana daga 20 ga watan Satumba, sai dai manyan gyare-gyare da kuma sauya wasu kayan aiki ka iya sanyawa a rufe ta tsawon wasu watanni.

Da yake mayar da martani kan rahoton, Anthony Chiejina, ya bayyana ikirarin a matsayin “labarin ƙarya” yana mai ɗiga ayar tambaya kan dalilin da Reuters zai yi amfani da kalmar ‘yiwuwa’ a rahoton idan har yana da tabbaci kan shirin rufewar matatar, kamar yadda ya shaida wa jaridar Punch a ranar Lahadi.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda