Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa Boko Haram ta kai mummunan hari a garin Darajamal na ƙaramar Hukumar Bama a daren Juma’a, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 63. Harin ya girgiza al’ummar jihar baki ɗaya.
Daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai sojoji guda biyar da kuma fararen hula kusan 58. Waɗannan fararen hula da aka halaka sun taba yin gudun hijira saboda hare-haren Boko Haram a baya, sai dai bayan al’amura sun lafa, sun dawo Darajamal kimanin watanni biyu da suka gabata kafin a sake afka musu.
A ranar Asabar, Gwamna Zulum ya ziyarci garin domin jajanta wa iyalan da abin ya shafa. Ziyararsa ta kasance wata babbar alama ce ta nuna goyon baya da kuma ta’aziyya ga al’ummar da ta fuskanci wannan mummunan hari.
A lokacin ziyarar, Zulum ya gana da shugabannin yankin, inda ya bayyana baƙin cikinsa tare da jajanta musu. Ya ce gwamnatin jihar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tallafa musu da kuma ƙarfafa musu gwiwa.
Da yake magana da manema labarai, gwamnan ya bayyana cewa al’ummar Darajamal sun koma ne domin gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum, amma abin takaici, an sake kai musu hari. Ya ce manufar ziyararsa ita ce ta’aziyya da kuma ƙarfafawa jama’ar yankin gwiwa.
- An Kashe Mutane 6, An Sace Sama da 250 A Cikin Kwanaki 3 A Katsina
- Matasa Sun Kashe Yan Bindiga 6 Sun Sha Alwashin Kare Kansu
Zulum ya kara da cewa rahotannin da aka tabbatar sun nuna cewa an rasa rayukan mutane 63, inda da dama daga cikinsu fararen hula ne.
Wannan hari ya ƙara bayyana irin kalubalen tsaro da ake fuskanta a yankin.
Baya ga haka, gwamnan ya yi kira da a gaggauta tura sabbin jami’an Forest Guards da aka horas domin su taimaka wa dakarun soja wajen kare al’ummar yankin.
Ya ce wannan mataki zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan ta’adda a yankunan karkara.
Hakazalika, Zulum ya jaddada bukatar haɗa kai tsakanin gwamnati, jami’an tsaro da kuma al’umma wajen yaki da ta’addanci.
Ya ce nasara a wannan yaki ba za ta tabbata ba sai idan kowa ya bada gudummawarsa.