An Buɗe Taron Sauyin Yanayi Na Afrika A Addis Ababa

An fara taron sauyin yanayi na Afirka na biyu a ranar Litinin a birnin Addis Ababa, inda ake sa ran shugabannin ƙasashe 45 da kusan wakilai 25,000 za su halarta.

Wannan taro na tsawon kwana biyu, wanda Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka da gwamnatin Habasha ke goyon baya, na da nufin nuna hanyoyin magance matsalolin yanayi da suka dace da nahiyar Afirka.

Haka kuma, taron na neman karfafa murya guda daya ta Afirka a fagen duniya kan rage illolin sauyin yanayi, tare da bunkasa tsare-tsaren da ke da amfani ga kasashen Afirka musamman kafin taron COP da za a gudanar a Brazil a watan Nuwamba mai zuwa.

Ana sa ran taron zai taimaka wajen haɗa kan ƙasashen Afirka wajen fitar da manufofi da shirye-shirye na hadin gwiwa kan yanayi.

Post masu alaƙa

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano

Babachir Lawal ya fita daga ADC

DSS ta kama mutane 5 da ake zargi da sace ɗaliban makarantar St. Mary’s Pipiri a jihar Neja