kwamatin da gwamnatin jihar Kano ta kafa kan yankewa ma’aikatan jihar albashinsu na watan Fabarairun shekarar 2025 ya gabatar da rahotonsa ga Gwamna.
A yayinda yake karin haske a taron manema labarai da ya kira, sakataren gwamnatin Kano,Alhaji Umar Faruq Ibrahim ya tabbatar dacewa, gwamnatin Kano ta dauki dukannin matakan daina yankewa ma’aikatan Kano albashinsu.
Yace a yanzu haka rahotan kwamatin yana gaban gwamna Yusuf domin yin nazari.
Sakataren gwamnatin jihar Kano yace , yanke albashin zai kasance kodai matsala ce daga Na’ura mai kwakwalwa ko Kuma daga hali na dan Adam.
- An Garkame Majami’u 50 Kan Rashin Bin Doka A Kamaru
- ‘Yan Sandan Sun Kama Waɗanda Ake Zargi Da Cire Kan Almajiri A Adamawa
Kafar yada labarai ta TST Hausa ta rawaito cewa, a ranar 27 ga watan Fabarairun shekarar 2025 ne gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamiti mai ƙarfi domin bincikar rahotannin da ke nuna cewa ana rage wa wasu ma’aikatan gwamnati albashi ko kuma ba a biyansu gaba ɗaya.
Gwamnan ya bayyana hakan a matsayin cin zarafi da take haƙƙoƙin ma’aikata, yana mai jaddada cewa ba zai amince da irin wannan dabi’a ba.
A karin hasken da Sakataren gwamnatin Kano,Alhaji Faruq Ibrahim yayi ,ya hakurkurtar da ma’aikatan Kano akan abinda ya faru na yanke musu albashi.
A game da gano ma’aikatan bogi,yace duk ma’aikacin da baije an tantanceshi ba ,to ya dauki kansa a matsayin korarren ma’aikaci.
A cikin Rahoton da kwamatin ya gabatarwa gwamnatin Kano, Sakataren gwamnatin jiha Alhaji Umar Faruq Ibrahim yace an gano ma’aikatan jabu da dama dake karbar albashi duk wata.
Yace duk ma’aikatan da suka kasa zuwa a tantancesu to sune ake zargi suna karbar albashi ba bisa ka’ida ba.