• Home  
  • Matsalar Rashin Tsaro Na Neman Kassara Arewacin Najeriya– Ƙungiyar Tuntuba Ta Arewa
- Babban Labari - Labarai

Matsalar Rashin Tsaro Na Neman Kassara Arewacin Najeriya– Ƙungiyar Tuntuba Ta Arewa

Ƙungiyar Tuntuba Ta Arewa ta ACF, ta nuna damuwarta kan yadda matsalar rashin tsaro ke neman kassara yankin Arewacin Najeriya, Shugaban Kwamitin Amintattun ƙungiyar Alhaji Bashir Muhhamd  Ɗalhatu Wazirin Dutse ne ya bayyana hakan a yayin ziyarar da ƙungiyar takai jihar Borno. Alhaji Bashir Ɗalhatu ya ƙara da cewa yanayin yadda ake samun ƙaruwar tashe-tashen […]

Ƙungiyar Tuntuba Ta Arewa ta ACF, ta nuna damuwarta kan yadda matsalar rashin tsaro ke neman kassara yankin Arewacin Najeriya, Shugaban Kwamitin Amintattun ƙungiyar Alhaji Bashir Muhhamd  Ɗalhatu Wazirin Dutse ne ya bayyana hakan a yayin ziyarar da ƙungiyar takai jihar Borno.

Alhaji Bashir Ɗalhatu ya ƙara da cewa yanayin yadda ake samun ƙaruwar tashe-tashen hankula a yankin na Arewa abun tsoro ne.

ACF ta nemi mahukunta da su ɗauki matakan gaggawa da zasu kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ya addabi yankin.

Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya ita ce babbar barazana da take addabar yankin. Musamman Jihohin Sakkwato da Zamfara da Katsina.

A baya baya ne dai Ƙungiyar ta dattawan Arewa ta gudanar da wani taro a Kaduna inda aka haɗa kan manyan Arewacin Najeriya domin nemo bakin zare da mafita ga yankin.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai