Matsalar tsaro ce ke gurgunta tattalin arzikin Najeriya – Kalu

Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, ya ce matsalolin tsaro da ake fama da su a sassan Najeriya na hana ƙasar cimma burinta na gina tattalin arziki mai ƙarfi wanda zai inganta rayuwar al’umma.

Ya ce sai an ba fannin tsaro muhimmancin da ya kamata idan ana son samun ingantaccen tattalin arziki a Najeriya.

“Kasar nan tana buƙatar bunƙasa tattalin arziki domin a samu kuɗi, wadata da kyakkyawar rayuwa ga ƴan Najeriya. Wannan shi ne abin da ƙasar ke buƙata,” kamar yadda Kalu ya faɗa a wajen taron ƙaddamar da wasu ayyuka a jihar Sokoto.

Tsohon gwamnan ya buƙaci a ɗauki tsauraran matakai domin magance matsalolin tsaro, ida ya ce hakan zai taimaka wajen samar da ci gaba sosai a fannin tattalin arziki.

Post masu alaƙa

Tinubu ya tura Shettima ya wakilci Najeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya a Amurka

APC ta ƙalubalanci Atiku ya yi bayani dalla-dalla kan yadda zai dawo da tallafin mai

NAHCON ta musanta zargin karkatar da kujerun Hajjin 2027