Messi Ya Kafa Sabon Tarihin Cin Ƙwallaye A Gasar Kofin Duniya

Tauraron ɗan wasan Argentina, Lionel Messi, ya zama ɗan wasan da ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin gasar Kofin Duniya bayan ya ci ƙwallonsa ta 17 da 18 a wasan da ƙasarsa ta buga da Austria a ranar Litinin.

Messi ya karya tarihin tsohon ɗan wasan Jamus, Miroslav Klose, wanda yake riƙe da kambun da ƙwallaye 16.

Kyaftin ɗin na Argentina ya kamo tarihin da Klose ya kafa ne a makon da ya gabata yayin da ya ci ƙwallaye uku rigis a wasan da suka doke Algeria da ci 3-0 a babbar gasar tamaular da suke fafutikar kare kambunsu.

A wasan da Austria, Messi ya zura ƙwallayen ne a minti na 38 da kuma 95, lamarin da ya sa magoya baya suka ɓarke da sowa a filin wasan na Arlington da ke Jihar Texas.

Tun a minti na tara da soma wasan ne Messi ya ɓarar da bugun fenariti kafin daga bisani ya samu nasarar saka sunansa cikin kundin tarihin gasar.

Messi mai shekara 38 yana buga gasarsa ta shida ta Kofin Duniya, bayan wadda ya fara halarta tun a shekarar 2006.

Ya zuwa yanzu Messi ya jefa ƙwallaye 122 a wasanni 201 da ya buga wa Argentina.

Wannan nasara ta ƙara ƙarfafa fatan Argentina na zama ƙasa ta farko tun bayan Brazil a shekarar 1962 da za ta lashe kofin duniya sau biyu a jere.

Bayan Messi da Klose, tsohon tauraron Brazil Ronaldo Nazario ne ke matsayi na uku da ƙwallaye 15, yayin da Gerd Müller da Kylian Mbappe ke biye da ƙwallaye 14 kowannensu.

Argentina ta tabbatar da samun gurbin zuwa zagaye na gaba da wannan nasara da ta yi nasara a kan Austria, kuma za ta kammala a saman rukunin J idan Algeria ta hana Jordan samun nasara a wasan da za su buga washegari.

Post masu alaƙa

Kwankwaso da Dickson sun gana kan rikicin NDC a Kano

An gurfanar da mutane 24 kan zargin kashe Ummulkhairi a Mararrabar Jos, Kaduna

Sojoji sun ceto mutane 47 da ISWAP ta yi garkuwa da su a Borno