Rundunar yan sandan Nijeriya ta gayyaci Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, don amsa wasu tambayoyi kan wani lamari da ya faru a lokacin bikin Sallah a Kano.
Idan ba a manta ba a ranar 28 ga watan Maris 2025 , Muhasatvr.ng ta ruwaito mu ku cewa hukumomin tsaron jihar Kano, sun sanar da dakatar da bukukuwan hawan sallah karama.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori , ne ya jagoranci sanarwar a wani taron manema labarai da ya gudana a shelkwatar rundunar a unguwar Bompai.
Kwamishinan yan sandan ya ce, a matsayin su na jami’an tsaro sun zauna tare da gwamnatin jihar Kano, inda suka basu shawarar cewa yin hawan sallar zai kawo matsaloli na rashin tsaro , da kuma rasa rayuka da dukiyoyin jama’a, shi yasa suka dauki matakin hana yin hawan sallar baki daya.
CP Bakori ya kara da cewa dukkan hawan sallah an dakatar da su kuma babu wanda za a bari ya hau doki yana yawo don yin kilisa.
- An Yi Jana’izar Tsohon Sakataren Gwamnatin Borno Alh. Muh’d Kagu
- Jihar Bauchi Ta Samu Tallafin Riga-kafin Cutar Folio Daga UNICEF
Sai dai a lokacin da tawagar mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sunusi ii, suke dawo wa daga sallar idi, da misalin karfe 12:40pm na rana, aka samu rahotan caka wa wani jami’in bijilanti wuka, mai suna Surajo Rabi’u, Wanda hakan ya Yi sanadiyar rasa ransa, sannan aka raunata wani jami’in bijilantin Mai suna Aminu Sulaiman Kofar Mata, inda rundunar ta kama matashin da ake zargi mai suna, Usman Sagiru, dan Shekaru 20 nazaunin unguwar Sharifai , don fadada bincike akansa.
A wasiƙar gayyatar da rundunar yan sandan ta kasa ta yiwa Sarki Sunusi, mai dauke da sa hannu Kwamishina yan sandan sashin tattara bayan sirri, CP Olajide Ibitoye,sun bukaci sarkin da ya bayyana a ranar Talata 8 ga watan Afrilu da misalin ƙarfe 10 na safe, da nufin gudanar da cikakken bincike kan yadda lamarin ya faru a ranar salla da kuma gano musabbabin rikicin da aka samu.
Sufeta Janar na yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun, ne ya umurci sashen tattara bayanan sirri da ta karbe fayil ɗin binciken tare da gayyatar Sarkin zuwa Abuja domin amsa tambayoyi.
Haka zalika a ranar 30 ga watan maris 2025 rundunar yan sandan Kano ta gaiyaci shamakin Kano, Alhaji Wada Isiyaku, don gudanar da bincike akansa dangane da abunda ya faru a ranar idin sallah.
Kafin hukumomin tsaron su hana bikin sallar , gwamnan jihar na Kano , Abba Kabir yusuf, ya nemi dukkan masarautun Kano huɗu ƙarƙashin jagorancin Sarki Muhammadu Sanusi II da su shirya aiwatar da hawan salla.
Sanarwar haramcin hukumomin tsaron, ta zo ne kwana ɗaya bayan Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero , ya sanar da soke shirinsa na yin hawan kamar yadda ya tsara tun farko, yayin da yake ci gaba da bayyana kansa a matsayin sarki duk da matakin gwamnatin Kano na sauke shi.
Haka zalika, shi ma Sarki Sanusi ya aika wa hukumomin tsaron jihar wasiƙa yana mai sanar da su shirinsa na gudanar da bikin al’adar da aka saba yi duk shekara, amma daga bisani ya sanar da janyewa.
Sanarwar hukumomin tsaron ta jaddada cewa duk Wani Abu da ya danganci hawan sallah a fadin jihar an haramta gudanar dashi da kuma aiyukan daba.
SP Abdullahi Kiyawa kakakin yan sandan Kano, ya ce duk Wanda aka kama ya dauko Wani Abu ko Yunkurin tayar da hankalin al’umma za a kama shi Kuma doka zata yi aiki akansa.
Ana dai zargi Sarki Muhammadu Sanusi , da yin hawa ranar Sallah da hawan daushe da kuma Hawan Nasarawa inda ya kai ziyara ga gwamnan jihar Kano, amma ba tare da an yi amfani da dawakai ba.
Ricikin masarautar Kanon ya dauki sabon salo tun lokacin da gamnatin Kano ta rushe masarautun da gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta samar tare da cire sarki na 15 Aminnu Ado bayero, inda ta yi sabuwar doka tare da nada Sarki Sunusi na II a matsayin sarkin Kano.
Ko a shekarar 2024 sai da gwamnatin Jihar Kano ta soki rundunar ’yan sandan jihar kan zargin ta da yin watsi da umarnin gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, game da bikin hawan sallah a jihar.
A wani taron manema labarai, babban lauyan jihar, Haruna Isah Dederi, ya yi tambaya kan dalilin da ya sa Kwamishinan ’yan sandan jihar ya hana gudanar da bukukuwan hawan sallah babba ba tare da tuntubar gwamnan jihar ba.
Ya jaddada cewa gwamna shi ne babban jami’in tsaro don haka ya kamata a ce shi ne zai yanke irin wannan hukunci.
An dade ana nuna wa juna yatsa tsakanin gwamnatin Kano da kuma rundunar yan sanda, saboda wasu dalilai da bangarorin biyu ke ganin basu yi daidai da tsarin dokar kasa ba, wanda masu nazari kan al’amuran yau da kullum ke ganin koma baya ne ga ci gaban jihar da kuma al’ummar ta.