Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta karɓi baƙuncin jami’an kwalejin leken Asiri ta Sojojin Nijeriya.

 

Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta karɓi baƙuncin jami’an kwalejin leken asiri ta Sojojin Nijeriya da ke Karu a Abuja, a wata ziyara da suka kai hedikwatar rundunar da ke Bompai, domin nazari kan amfani da bayanan sirri wajen dakile rikice-rikice da inganta tsaro.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

A yayin ziyarar, Mataimakin Kwamandan Kwalejin, Group Captain A.O. Adisa, wanda ya wakilci Kwamandan Kwalejin, Air Commodore Usman Mainasara Bugaje, ya ce sun zaɓi Rundunar ƴan sandan Kano domin ƙara koyo da fahimtar dabarun da take amfani da su wajen tafiyar da harkokin tsaro.

A nasa bangaren, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa rundunar na aiki ne tare da al’umma domin samun bayanan sirri da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, tare da horar da jami’anta da yaƙi da laifukan intanet, wayar da kan jama’a, da kuma ci gaba da aiwatar da shirin “Operation Kukan Kura” domin dakile daba da sauran miyagun laifuka.

Bayan tattaunawa, Group Captain A.O. Adisa ya yaba wa CP Ibrahim Adamu Bakori, da jami’an rundunar bisa ƙoƙarinsu wajen tabbatar da tsaro a Kano.

A madadin mahalarta ziyarar, DSP A.H. Runka ya gode wa CP Ibrahim Adamu Bakori da rundunar ƴan S=sandan Kano bisa kyakkyawar tarba da kuma ilimin da suka amfana da shi a yayin ziyarar.

Post masu alaƙa

Kwankwaso da Dickson sun gana kan rikicin NDC a Kano

An gurfanar da mutane 24 kan zargin kashe Ummulkhairi a Mararrabar Jos, Kaduna

Sojoji sun ceto mutane 47 da ISWAP ta yi garkuwa da su a Borno