Shugaban Jamiyyar APC na kasa, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya ce sun karɓi tuban Sanata Ali Ndume tun da ya fahimci kuskurensa a taƙaddamar da ta taso har aka samu saɓani tsakaninsa da jam’iyyar.
A baya dai Jamiyyar APC ta aikewa majalisar dattijan kasar nan takardar korafi akan sanatan, wanda hakan ya yi sanadiyyar sauke shi daga mukaminsa na bulalaliyar majalisa.
Ganduje ya ce, “Mun karbi tuban Ndume, kuma za mu sake rubutawa majlisa takarda dan sake duba matakin da ta dauka a kanshi”
Ali Ndume shine sanata mai wakiltar Borno ta kudu, yana cikin ‘yan gaba-gaba wajen sukar salon tafiyar da mulkin da jamiyyarsa ke jagoranta.
Hakan ce tasa Shugabancin jamiyyar ya aike wa majalisar dattawan kasar nan, karkashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio wasiƙar ƙorafi akan yadda Sanata Ndume ke kwayewa jam’iyyar baya.
Wanda sakamakon hakan ne ya sa majalisar yanke hukuncin sauke Ali Ndume daga mukaminsa na mai tsawatarwa.