An wayi gari da hazo a sassan jihar Kano a safiyar Lahadi, inda ba a iya hango wanda ke sama da mita 500.
A irin wannan yanayi, fitowa wuraren aiki kan yi wa mutanen da basu da mota wahala sakamakon sanyi da iskar da ke kaɗawa.
Ana sa ran za a cigaba da samun irin wannan yanayi har zuwa ƙarshen watan ɗaya zuwa farkon watan biyu na shekarar 2025 kamar yadda aka saba.
A irin wannan yanayi, masu cutar sarƙewar numfashi na fuskantar barazana, sakamakon yanayin bai dace da buƙatar lafiyarsu ba.
Hakan ta sa, ma’aikatan lafiya ke shawartar jama’a su riƙa kula da lafiyar su domin kaucewa hatsarin da ke tattare da ƙurar da ke tashi.