Mutane sama da 1,000 sun kamu a da cutar Ebola a Congo

Cutar Ebola ta kama sama da mutane dubu daya a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, yayin da barkewar cutar ta bazu zuwa sansanin ‘yan gudun hijira na uku, sannan ta yi sanadin mutuwar wata yarinya yar kimanin watanni 18.
Gwamnatin Kongo ta tabbatar da cewa adadin mutanen da suka mutu ya kai 254.
Yaduwar cutar cikin sauri a larduna uku na gabashin Congo ya sa ƙwararrun kiwon lafiya na Afirka suka yi gargadin cewa barkewar na iya wuce mummunar annobar da ta kashe fiye da mutane 11,000 a yammacin Afirka tsakanin shekarun 2014 zuwa 2016.
Wani rahoton masana kiwon lafiya daga Kongo ya bayyana cewa an gwada jaririyar mai kimanin watanni 18 kan cutar Ebola a ranar 14 ga watan Yuni a sansanin ‘yan gudun hijira na Hungbe, kuma ta mutu kafin a samu sakamakon gwajin da ya tabbatar da cewa tana dauke da cutar a washegari.
Rahoton ya ce yarinyar ta fara fama da zazzabi fiye da mako guda kafin haka, kuma an kai ta da ƙafa zuwa cibiyoyin lafiya biyu daban-daban inda aka ba ta maganin kashe ƙwayoyin cuta (antibiotics), kafin daga bisani a yi mata gwajin Ebola.
Akalla mutane 107 ne suka yi hulɗa da ita, ciki har da ‘yan uwanta, ma’aikatan lafiya da wasu mutane daga wasu sansanonin ‘yan gudun hijira.
Dr. Emmanuel Musingusi Bulemu, wani jami’in lafiya a yankin Nizi da keCongo, ya ce akwai ƙarancin wuraren ware masu fama da cutar.

Post masu alaƙa

Kwankwaso da Dickson sun gana kan rikicin NDC a Kano

An gurfanar da mutane 24 kan zargin kashe Ummulkhairi a Mararrabar Jos, Kaduna

Sojoji sun ceto mutane 47 da ISWAP ta yi garkuwa da su a Borno