Kotun tarayya ta ƙi sassauta belin El-Rufai yayin da DSS ta kammala gabatar da hujjoji

Kotun tarayya da ke sauraron shari’ar zargin sauraron wayoyi ba bisa ka’ida ba da ake yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta ƙi amincewa da buƙatar da aka gabatar na neman sassauta sharuɗɗan belinsa.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, ta bayyana cewa sharuɗɗan beli masu tsauri da aka kafa tun farko za su ci gaba da aiki. Waɗannan sharuɗɗan sun haɗa da buƙatar masu tsaya masa su kasance manyan ma’aikatan gwamnati a matakin daraja ta 17, tare da mallakar kadarori a yankunan Maitama ko Asokoro, da kuma takardar shaida daga Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna. Ta ce har yanzu akwai mutanen da suka cancanci cika waɗannan sharudda.
A zaman kotun na ranar, Hukumar Tsaro ta Ƙasa (DSS) ta sanar da gabatar da hujjoji a kan El-Rufai, inda ta tabbatar cewa ba za ta ƙara kiran wasu shaidu ba.
Lauyan dake kare El-Rufai, Paul Erokoro, ya bayyana aniyar su ta shigar da “buƙatar rashin hujja,” inda suke cewa masu gabatar da ƙara sun gaza kawo hujjoji masu ƙarfi da za su tabbatar da tuhumar.
Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 22 ga Satumba, 2026, domin duba buƙatar rashin hujja tare da ci gaba da shari’ar.

Post masu alaƙa

Kwankwaso da Dickson sun gana kan rikicin NDC a Kano

An gurfanar da mutane 24 kan zargin kashe Ummulkhairi a Mararrabar Jos, Kaduna

Sojoji sun ceto mutane 47 da ISWAP ta yi garkuwa da su a Borno