Na Bar Rundunar Sojin Najeriya Cikin Farin Ciki Da Alfahari

Tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce ya bar aiki da rundunar sojin ƙasar cikin farin ciki da alfahari.

Yayin da yake jawabi a wani ƙwarya-ƙwaryar bikin da aka shirya masa kan bankwana da aikin soji a Abuja, babban birnin ƙasar, Janar Musa ya ce ya yi iya ƙoƙarinsa wajen bauta wa Najeriya da gaskiya da aminci.

Tsohon babban hafsan sojin ƙasar, wanda ya shafe shekaru da dama a aikin sojin ƙasar, ya ce hidimarsa cike take da jajircewa da sadaukarwa.

“Yayin da nake cire kayan soja a yau, ina yin hakan cike da alfahari, saboda irin gudummawar da na bayar wajen kare ƙasata,” in ji shi.

Janar Musa ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa damar da ya ba shi don jagorantar rundunar tsawon fiye da shekaru biyu, yana mai kira ga dakarun ƙasar su bai wa sabon shugaban da sauran shugabannin rundunonin sojin ƙasar cikakken goyon baya.

“Duk da cewa na bar aikin soji yau, ba zan daina ƙaunar ƙasata ba. Har yanzu soja ne ni a zuciya, kuma ɗan ƙasa ne mai kishin Najeriya,” in ji Janar Musa.

A makon da ya gabata ne Shugaba Tinubu ya sake fasalin manyan hafsoshin tsaron ƙasa, inda ya maye gurbin Janar Musa da Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon babban hafsan tsaron ƙasar.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda