Na fice daga PDP ne don kare kaina – Adeleke

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya kare matakin da ya ɗauka na ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar AP, yana mai cewa ya sauya sheƙa ne domin kare kansa da kuma tabbatar da zaman lafiyar jihar.

Adeleke, yayin da yake magana a gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, ya ce bai yi watsi da PDP ba, wacce har yanzu yake girmamawa, sai dai ya zaɓi fifita ɗorewar ci gaban da ake samu a Osun.

Ya ce:“Ba gaskiya ba ne cewa na yi watsi da PDP. Ina son PDP, amma dole ne in kare kaina.

Dole ne in tabbatar na kare jihata saboda kyawawan ayyukan da muke yi domin mu ci gaba.”

Adeleke ya shiga jam’iyyar AP ne a ranar Talata bayan ya fice daga PDP, jam’iyyar da ta kai shi mulki a zaɓen gwamnan jihar na 2022.

A ranar Laraba ne ya samu tikitin takarar gwamna a karkashin sabon jam’iyyarsa ta AP.

Yanzu haka zai kara da ‘yan takara daga APC, PDP, da kuma jam’iyyar hɗaka ta ADP a wani zabe da ake sa ran zai kasance mai matukar tasiri ga makomar siyasar sa.

Dangane da damuwar cewa takara a karkashin jam’iyya mara karfi na iya rage masa kuri’u a zaben 2026, Adeleke ya nuna kwarin gwiwa, yana mai cewa ayyukan da ya gudanar a mulkinsa za su samar masa wa’adin mulki na biyu.

Post masu alaƙa

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda

‘Talauci ya faɗo daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto