Najeriya na buƙatar ƙarin dala biliyan 410 domin cimma burinta na sauyin makamashi da rage hayakin da ke haddasa ɗumamar yanayi zuwa shekarar 2060.
Mai ba shugaban ƙasa shawara a Ofishin mataimakin Shugaban Ƙasa kan ayyukan raya ƙasa, Hon. Musaddiq Mustapha Adamu, ya ce kuɗaɗen za su taimaka wajen samar da makamashi mai tsafta da kuma gina ababen more rayuwa masu jure wa sauyin yanayi.
Ya ce gwamnati ita kaɗai ba za ta iya samar da dukkan kuɗaɗen da ake buƙata ba, don haka akwai buƙatar haɗin gwiwar bankuna, masu zuba jari da kamfanoni masu zaman kansu.
Ya ƙara da cewa masu zuba jari na buƙatar cikakken bayani kan manufofin gwamnati, hanyoyin samun kuɗaɗen shiga daga ayyukan, da kuma yadda za a raba haɗarin da ka iya tasowa.
A nasa ɓangaren, wakilin mataimakin shugaban kasa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, ya ce lokaci ya yi da za a daina tattaunawa kawai, a mayar da hankali kan aiwatar da ayyukan da aka tsara.
Ya ce akwai buƙatar sauƙaƙa hanyoyin samun lasisi da amincewar hukumomi, tare da rage haɗarin da masu zuba jari ke fuskanta.
Haka kuma, ya ce ya kamata a samar da damar da kuɗaɗen fansho da inshora za su saka jari a manyan ayyukan more rayuwa na dogon lokaci.
Taron DIN Summit, wanda Ofishin mataimakin shugaban kasa tare da National Council on Climate Change suka shirya, ya tattauna hanyoyin jawo ƙarin jari da kuma samar da ababen more rayuwa masu ɗorewa a Najeriya.