Rundunar yan sandan jihar Kano ta sake jaddada haramcin hawan dawakai ko dabbobi da sunan “Da-ba.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta sake jaddada haramcin hawan dawakai ko dabbobi da sunan “Da-ba” a fadin jihar.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce haramcin ya shafi kowa da kowa, ba tare da la’akari da matsayi ko mukami ba.

CP Bakori ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da hukumomin tsaro suka gudanar a hedikwatar ’yan sanda da ke Bompai, Kano, a yau Juma’a 2 ga Oktoba, 2026.

Ya ce gwamnatin jihar ta dauki matakin ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro, domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayukan al’umma.

Kwamishinan ya ce duk wani mutum, ma’aikata ko kungiya da ke bukatar gudanar da hawan dawakai ko dabbobi a jihar, dole ne ya nemi izini a rubuce daga Ofishin kwamishinan yan Sandan Jihar Kano, a kalla sa’o’i 72 kafin lokacin gudanar da taron.

Ya ce hakan zai bai wa jami’an tsaro damar tantance yanayin tsaro da kuma yin shirye-shiryen da suka dace domin kare jama’a.

CP Bakori ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su bi dokokin tsaro tare da bai wa jami’an tsaro cikakken hadin kai.

Ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro za su ci gaba da daukar matakan da suka dace domin tabbatar da doka, zaman lafiya da oda a fadin Jihar Kano.

Post masu alaƙa

Shugaba Tinubu ya lissafa nasarorin da ya samu a ƙasa da shekaru huɗu

Tinubu ya koma gida bayan shafe makonni yana hutu a Faransa

Tinubu na kan hanyar komawa Najeriya bayan kammala hutun aiki