Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya lissafo abubuwan da ya bayyana a matsayin nasarorin tattalin arzikin Najeriya tun lokacin da ya karɓi ragamar mulki shekaru uku da rabi da suka gabata.
A jawabin da ya yi na ranar cikar Najeriya shekaru 66 da samun ‘yancin kai, shugaban ya ce ƙasar ta fara ganin alamun ingantuwa a fannin tattalin arziki.
Ya ce tattalin arzikin ƙasar ya bunƙasa da sama da kashi huɗu cikin ɗari a shekarar 2026, tare da gudunmawar da bangaren man fetur da kuma waɗanda ba na man fetur ba suka bayar.
Haka kuma ya ce an rage satar danyen mai, yayin da hauhawar farashi ta ragu sosai daga kololuwar matsayin da ta kai a baya.
Bugu da ƙari, Tinubu ya bayyana cewa an sake gina asusun ajiyar kuɗaɗen ƙasar na waje, kasuwar musayar kuɗaɗen ƙetare ta samu daidaito, sannan Najeriya ta samu sama da dala biliyan shida daga fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba a shekarar 2025, wanda ya bayyana a matsayin mafi girma da ƙasar ta taɓa samu a tarihinta.