Najeriya ta bayyana ra’ayinta game da rikicin Falasdinawa da Isra’ilawa

Gwamnatin Najeriya ta ce ya kamata a aiwatar da tsarin samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu wato kasar Falasdinawa da ta Isra’ila don a tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Gabas Ta Tsakiya.

Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar ya ce rikicin ya jefa mutanen da ba su ji ba su gani ba cikin mawuyacin hali, yana mai kira ga Isra’ila ta bari a shiga Gaza da kayan agajin jinkai. Ministan ya jaddada kira a yi gaggawar tsagaita wuta a yakin Isra’ila da Falasdinawa

Ya ce dole ne bangarorin biyu su kiyaye ‘yancin dan Adam da kuma  dokokin jinkai na kasashen duniya wadanda suka bukaci a kare lafiyar fararen-hula a yayin da ake rikici.

Post masu alaƙa

2027: ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki

Zaɓen 2027: Rundunar yan sanda jihar Kano ta ba da tabbacin tsaro,tare da yin gargaɗi kan yada labaran ƙarya

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.